Buhari ya gaji manyan matsaloli – Shugabannin G7

Shugabannin kasasshen masu Arzikin Masana’antu (G7) sun shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa Najeriya tana fuskantar manyan matsaloli a yanzu. Shugabannin bakwai na kasashen da suka fi karfin arzikin masana’antu da suka hada da Amurka da Jamus da Kanada da Faransa da Itakiya da Japan sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin Buhari za ta […]

Buhari ya gaji manyan matsaloli – Shugabannin G7
Buhari ya gaji manyan matsaloli – Shugabannin G7

Shugabannin kasasshen masu Arzikin Masana’antu (G7) sun shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa Najeriya tana fuskantar manyan matsaloli a yanzu.

Shugabannin bakwai na kasashen da suka fi karfin arzikin masana’antu da suka hada da Amurka da Jamus da Kanada da Faransa da Itakiya da Japan sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin Buhari za ta fuskanci manyan matsaloli daga hawanta gadon mulki.
Da suka magana a ranar Litinin bayan Shugaba Buhari ya gabatar musu da bukatun Najeriya, sun bayyana manyan matsalolin da karancin kudi da almubazzaranci da kuma karancin kwararrun sojoji da ingantattun kayan yaki.
Shugabannin da G7 sun ce wadannan manyan matsaloli da suka fuskantar Najeriya ba Buhari ne ya jawo sub a.
Wata sanarwa da Babban Mai taimaka wa Shugaban kasa kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu ta ce kasashen masu karfin masana’antun sun yi alkawarin ba Shugaba Buhari goyon bay== da tallafa masa bayan da suka gamsu da “hanyar da ya zama Shugaban kasa da kuma dimbin kalubalen da gwamnatin da yake jagoranta take fuskanta wadanda ba shi ya jawo sub a, musamman ma kokarinsa na magance matsalar Boko Haram,” inji sanarwar.
Shehu ya ce, bayan Shugaba Buhari ya gabatar da bukatun Najeriya da shugabannin G7 din sun bayyana masa suna sane da amincewa da shi da kuma dimbin bukatun da jama’a ke da su kan gwamnatinsa. Sun yaba kan yadda ya samu nasarar a zaben da aka bayyana da mafi kyau a tarihin zaben kasar nan, sai dai sun nuna damuwa da dimbin kalubalen da gwamnatinsa ta iske.
Ya ce game da matsalar tsaro da Boko Haram ke haifarwa da ta tsallake iyakar Najeriya tana shafar kasashen yankin, shugabannin G7 din sun yarda cewa babu wata da za ta iya magance ta ita kadai.
Mukarrabin Shugaban kasar ya ce shugabannin G7 sun yaba wa Shugaba Buhari kan tuntubarsu da kuma makwabtan Najeriya cikin mako daya da kama ragamar mulkinsa. Ya ce, “Lura da hobbasar da ya yin a shawo kan matsalar, shugabannin sun yi alkawarin hada hannu da ba gwamnatin Buhari tallafi don magance manyan matsalilin da suke fuskantar Najeriya. Sun ba Buhari damar ya kawo irin abubuwan da gwamnatinsa take bukata, inda suka ba shi tabbacin, za su nazarci bukatun a daidaikunsu da kuma a kungiyance don bayar da tallafi.”
Ya kara da cewa; “Sun bukaci su san iri da girman matsalolin don sanin irin taimakon da za su bayar. Kuma sun ba Buhari tabbacin ‘G7 za su hada hannun da Najeriya.’ Kuma Shugaba Buhari wanda ya samu damar zama mutum na farko da ya yi jawabi ga taron G7 a tsakanin shugabannin da aka gayyata ya samu kyakkyawar tarba a wurin taron, inda ya dawo Najeriya a safiyar Talata 9 ga Yuni.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos