Buhari ya gana da Jonathan kan rikicin Mali

Buhari ya bukaci a kai zuciya nesa domin magance rikicin siyasar Mali.

Buhari ya gana da Jonathan kan rikicin Mali

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda shi ne wakili na musamman kuma mai shiga tsakani na ECOWAS a kasar Mali.

Buhari, a yayin ganawar da aka gudanar a Abuja, kan rikicin siyasa a kasar, ya yi kira ga bangarorin da su hada kai don samun zaman lafiya da hadin kan kasar.

A cewarsa, “Yanayin da ake cikin wanda mafi yawan sassan kasar ke hannun masu tayar da kayar baya na bukatar a yi yarjejeniya tare da maido da zaman lafiya, ba kara rura wutar rikicin ba.

“Ina kira ga duk masu ruwa da tsakin su hada kai domin samun zaman lafiya da tsaro a Mali.”

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce Jonathan ya yi wa shugaban bayanin halin da ake ciki a Mali bayan ganawa da manyan ’yan siyasa a gabanin taron shugabannin ECOWAS a karkashin Shugabancin Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana.

Ya kara da cewa taron shugabannin kasashen yankin ya zama wajibi don hanzarta samar da ingantacciyar hanyar warware matsalar da ke addabar kasar ta Yammacin Afirka.