Buhari ya gana da Sarkin Kano

Shugaba Buhari ya yi ganawar farko da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a Abuja

Buhari ya gana da Sarkin Kano

Shugaba Buhari a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja.

Hadimin Shugaban Kasa kan Daukar Hotuna Sunday Aghaeze, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa a daren Laraba Buhari ya gana da sarkin na Kano Alh. Aminu Ado.

Ganawar ita ce ganawa ta farko da Shugaban Kasar ya yi tun bayan nada shi a matsayin Sarkin Kano.

A ranar 9 ga watan Maris 2020, Gwamantin Jihar Kano ta tube tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kafin daga bisani ta maye gurbinsa da Sarki Aminu Ado Bayero.