Yadda dubban jama’a suka halarci jana’izar Sarkin Zazzau
Shugabannin Najeriya sun bayyana matukar kaduwa da rasuwar Sarkin Zazzau
Dubun dubatar mutane ne suka halarci jana’izar Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.
A ranar ce kuma aka kai gawarsa zuwa fadar sarkin da ke Zariya inda aka yi masa sallar janaza da yamma kafin a kai shi makwancinsa.
Shugabanni daga sassan Najeriya na ci gaba da bayyana jimaminsu game da rasuwar Sarki Shehu Idris.
- Buhari ya kadu da rasuwar
Shugaba Muhammadu Buhari, a sakon jana’izarsa ga Masarautar Zazzau da Gwamnatin Jihar Kaduna da jama’ar jihar ya roki Allah Ya jikan Sarkin da rahama Ya kuma ba wa daukacin jama’ar jihar hakurin jure rashin.
- Da karfe 5 za a yi jana’izar Sarkin Zazzau —El-Rufai
- Yadda ake juyayin rasuwar Sarkin Zazzau
- Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu
Buhari wanda ya bayyana matukar kaduwa da rasuwar ya ce, “Najeriya ta yi babban rashi da rasuwar Alhaji Shehu Idris —sarki mafi dadewa a kan karagar mulki— wanda ya yi amfani da matsayinsa wurin yada zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya.
“Sarkin Zazzau wanda ya hau mulki a 1975 ya yi amfani da mulkinsa wajen hidimta wa al’umma wajen ganin sun cimma manufofinsu”, inji sakon ta’aziyyar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar.
- Za da dade ana tunawa da shi —Majalisa
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, a sakonsa na ta’aziyya ya jajanta wa jama’ar jihar Kaduna game da rasuwar..
“Marigayin ya yi amfani da basira da kuma darajarsa wajen kawo zaman lafiya da kuma ci gaban Masarautar Zazzau, a lokacin mulkinsa.
“Za a ci gaba da tunawa da shi saboda matsayinsa da gaskiyarsa da kuma soyayyar da ya yi wa mutanensa da son ci gabansu a lokacin da yake raye,” inji sakon da ya wallafa shafinsa na Twitter.
- JIBWIS ta yi ta’aziya
Shi ma Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shaikh Abdullahi Bala Lau, mika ta’aziyarsa game da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
“Ina amfani da wannan dama wajen mika ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Masarautar Zazzau da daukacin jama’ar Jihar Kaduna game da wannan babban rashi.
“Allah Madaukakin Sarki Ya jikan sa ya kuma sa Aljannah Firdausi ce makomarsa”, inji Sakon Shaikh Bala Lau.
- Katsina ta kadu da rasuwar Sarkin Zazzau
Gwamnan Jihar Katsina, wadda aka fitar daga Jihar Kaduna, Aminu Bello Masari ya ce rasuwar Sarkin Zazzau babbar rashi ce musamman “a lokacin da matsaloli suka dabaibaye Najeriya”.
Sakon ta’aziyyar Masari ta ce, “Rasuwar ta auku ne a lokacin da ake matukar bukatar kwarewarsa da sanayyarsa a duniya domin ganin Najeriya ta samu mafita daga matsalolin tsaro da tattalin arziki da tsaro da suka yi mata katutu.
“Ya yi amfani da fada-a-jinsa a ciki da wajen Najeriya wajen kare muradun kasa”, inji gwamnan.