Buhari ya goyi bayan tabbatar da ‘yancin Falasdinawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana goyon bayan kudirin Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya (OIC) na tabbatar da samun ‘yancin Falasdinawa. Shugaban ya fadi haka ne lokacin da yake karanta jawabi a madadin mambobin kungiyar na kasashen Afirka a wajen babban taron da aka gudanar a Makkah na kasar Saudiyya. A cikin jawabinsa ya ce, […]

Buhari ya goyi bayan tabbatar da ‘yancin Falasdinawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana goyon bayan kudirin Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya (OIC) na tabbatar da samun ‘yancin Falasdinawa.

Shugaban ya fadi haka ne lokacin da yake karanta jawabi a madadin mambobin kungiyar na kasashen Afirka a wajen babban taron da aka gudanar a Makkah na kasar Saudiyya.

A cikin jawabinsa ya ce, kasashen Afirka sun yaba da kokarin kungiyar ta OIC na tabbatar da ‘yancin Falasdinawa da kuma kawon karshen rikicin gabas ta tsakiya da aka shafe shekara da shekaru ana yin sa.

Ya ce kasashe mambobin kungiyar na fama da barazanar tsaro, da suka hada da ta’addanci da tsauttsauran ra’ayi da kuma rikicin ‘yan bindiga.

Yakara da cewa matsaloli ne da suka dade ana fama da su,  wadanda suke bukatar daukar matakan kawo karshensu gaba daya.

Ya yaba da ayyukan  OIC na shawo kan rikicin kasasahen Syria da Yemen da Libya da kuma rikicin Musulmin Rohinga tsiraru a Myanmar.

Shugaban ya ce kungiyar tana da tasiri sosai ga Najeriya da sauran kasashen Afirka, musamman Bankin Musulunci (IDB) a kan yadda yake tallafawa a fannin kasuwanci da noma,  fasaha da yaki da talauci a tsakannin mata da matasan Afirka.

Sannan ya ce kungiyar na bada taimako ga yaki da ta’addanci a kasashen yammcin Afirka da na tafkin Chadi da kuma Sahel.

Shugaban Saudiya Sarki Salman Bin Abdul Aziz Al-Saud shi ne ya jagoranci taron, inda kuma Shugaban Kasar Turkiya, Recep Erdogan ya kawo karshen wa’adinsa na shugabancin kungiyar.