Buhari ya himmatu wajen ganin bayan Boko Haram
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya himmantu wajen ganin bayan kungiyar Boko Haram, inda jim kadan da rantsar da shi a ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayar da umarnin a dage hedkwatar yaki da Boko Haram daga Abuja ta koma Maiduguri da ke Jihar Borno, har sai an ga bayan Boko Haram. Sannan a ranar […]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya himmantu wajen ganin bayan kungiyar Boko Haram, inda jim kadan da rantsar da shi a ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayar da umarnin a dage hedkwatar yaki da Boko Haram daga Abuja ta koma Maiduguri da ke Jihar Borno, har sai an ga bayan Boko Haram.
Sannan a ranar Litinin, rana ta farko da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara aiki ya gana da Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, domin jin halin da ake ciki game da matsalar ta Boko Haram.
Sai washegari Talata ya gana da manyan hafsoshin sojojin kasar nan da suka hada da Babban Hafsan Tsaro Iya Cif Mashal Aled Badeh da Hafsan Hafsoshin Sojan kasa, Laftana Janar Kenneth Minimah da Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Iya Mashal A. N. Amosun da Hafsan Hafsoshin Sojan Ruwa, Bayis Admiral U. O. Jibrin da kuma Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Solomon Arase, domin jin inda aka kwana game da yaki da Boko Haram din tare da tattauna yadda za a bullo wa lamarin.
Bayan kammala ganawar, manyan hafsoshin sun bayyana cewa za a mayar da hedkwatar yaki da Boko Haram zuwa Maiduguri kamar yadda Shugaba Buhari ya nema nan da dadewa ba, kamar yadda Hafsan Hafsoshin Sojin Ruwa Admiral Usman Jibrin ya shaida wa manema labarai a Defence House da ke Abuja bayan kammala ganawar tasu ta awa uku. A shekaranjiya Laraba kuma Shugaba Muhammdu Buhari ya kai ziyara Jamhuriyyar Nijar inda ya gana da Shugaban Mahammdou Issousfou duk a kokarin nemo hanyoyin magance matsalar Boko Haram din.
A jawabinsa lokacin da ya ziyarci Shugaba Mahamadou Issoufou a birnin Yamai, Shugaba Buhari ya ce sojojin Najeriya na da karfin da za su kawo karshen ayyukan masu tayar da kayar baya, ya ce shekara biyar kungiyar na aikata tu’annati, ya isa haka.
Shugaba Buhari wanda ke jawabi ga manema labarai tare da Shugaba Issoufou ya ce, “Muna duba wasu hanyoyi ta yadda za mu sauya salon yaki da Boko Haram.” Kuma ya ce sojojin Najeriya za su karbi yankunan da suke hannun sojojin Nijar bayan kwato su. Ya ce ya ziyarci Nijar ne domin neman goyon baya kan yadda za a hanzarta kawo karshen ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram. Kuma ya ce Najeriya za ta bukaci taimakon kasashen duniya domin sake gina yankunan da hare-haren Boko Haram suka lalata.
A nasa bangaren, Shugaba Mahammadou Issoufou ya ce matakin da gwamnatin Najerya ta dauka na mayar da cibiyar dakarun da ke yaki da ta’addanci zuwa Maiduguri zai taimaka wajen kawo karshen ayyukan Boko Haram.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma ziyarci kasar Chadi inda ya gana da Shugaba Idris Beby kan yadda za a kawo karshen matsalar ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram.
A yau Jumu’a ne ake sa ran Hafsan Tsaro Iya Cif Mashal Aled Badeh da manyan hafsoshin sojan kasa da na sama wato Janar Kenneth Minimah da Iya Mashal Adesola N. Amosun za su jagorancin manyan jami’an soja zuwa Maiduguri don bin umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na mayar da hedkwatar yaki da Boko Haram zuwa can har sai an kawo karshen matsalar Boko Haram.
Wasu majiyoyi sun ce sojin kasa da na sama da suke yaki kai-tsaye da Boko Haram ta sama da kasa suna da muhimmanci ga manufar Shugaba Buhari na ganin bayan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Shi ma Hafsan Hafsoshin Sojin Ruwa Bayis Admiral Usman Jibrin zai hade da manyan hafsoshin a Maiduguri a makon mai zuwa. Majiyar ta ce tuni an samar da ofisoshin wucin-gadi ga manyan hafsoshin da za su koma Maiduguri, sannan manyan kwamandojin da za su jagoranci yakin da suka hada da daraktan ayyuka da na samar da kayan yaki da na leken asiri da na labarai na sojan kasa da na sama da hedkwatar tsaro duk za su koma Maiduguri don kaddamar da yaki a kan Boko Haram.