Buhari ya isa Landan don neman magani
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan domin yin jinyar ciwon kunnen da ke damunsa. Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Shugaba Buhari zai yi hutun kwana 10 a birnin Landan, inda za a duba lafiyarsa. Har ila yau, sanarwar, mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara a […]

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan domin yin jinyar ciwon kunnen da ke damunsa.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce Shugaba Buhari zai yi hutun kwana 10 a birnin Landan, inda za a duba lafiyarsa.
Har ila yau, sanarwar, mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara a kan al’amuran yada labarai, Femi Adesina ta ce wani likitan da ya ƙware kan cututtukan da suka shafi kunne da hanci da maƙogwaro ne ya ba da shawara a sake duba shugaban domin gudun abin da ka je ya zo.
A jiya Lahadi ne wasu kafofin yaɗa labarai suka bayar da labarin cewa shugaban yana jinya, amma sai kakakin shugaban ya musanta hakan.