Buhari ya jagoranci kaddamar da ginin Cibiyar Kula da Lafiya ta Afirka a Abuja
Cibiyar dai za ta lakume sama da Dalar Amurka miliyan 300.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya jagoranci kaddamar da ginin Cibiyar Kula da Lafiya ta Afirka a Abuja.
Cibiyar, wacce za ta kasance muhimmiya a bangaren lafiya ana sa ran za ta kawo sauyi a fannin kiwon lafiya a Yammacin Afirka gaba daya, sannan za ta lakume sama da Dalar Amurka miliyan 300 yayin kammala wa.
- Kotu ta daure tsohon jami’in Kwastam kan fasakwaurin bindigogi
- Kotu ta sa ranar yanke hukunci kan ko Atiku ya cancanci tsayawa takara
Bankin Shige da Fice na Afirka (Afreximbank) ne tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Asibitin Kings College da ke London da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Wisconsin na Amurka da na Christies da ke birnin Manchester ne ke gudanar da aikin ginin cibiyar.
“Cibiyar za ta kunshi kwararan gadajen kwanciya guda 500, za ta yi aiki a bangarorin cututtukan daji da na zuciya da kuma cututtuka masu yaduwa. Kuma za ta magance karancin cibiyoyin kula da lafiya a Najeriya da kuma yankin Yammacin Afirka gaba daya,” cewar Shugaba Buhari.
A karshe ya yaba wa Ma’aikatun Cinki, Zuba Jari da Masana’antu, da ta Harkokin Waje da ta Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma ta Lafiya bisa jajircewarsu wajen ganin an tabbatar da wannan babban ci gaban.