Buhari ya je Daura bikin sallah
Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Daura da ke jihar Katsina inda ya zabi ya taka a kasa ta babban titin garin zuwa gidansa da ya cika makil da jama’a masu tarbansa. Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kan Yada Labari da Wayar da Kan Jama’a, Garba Shehu shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa […]
Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Daura da ke jihar Katsina inda ya zabi ya taka a kasa ta babban titin garin zuwa gidansa da ya cika makil da jama’a masu tarbansa.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kan Yada Labari da Wayar da Kan Jama’a, Garba Shehu shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya.
“Shugaban Kasa wanda Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ya tarbe shi yayin da ya sauka daga karamin jirgin sama ya taka a kasa har zuwa gidansa tare da dimbin al’ummar da suka tarbe shi. Yayin da Shugaban Kasa yake tafiya gidansa jama’a sai suka rika yin shewa suna murna suna cewa Baba ya dawo, baba oyoy”. Inji sanarwar.
Ya ce tun farko Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ne suka tarbe shi kafin a dauke shi a karamin jirgin helikwafta zuwa garin Daura.
Shehu ya ce Shugaban Kasar zai zauna tare da iyalansa a lokacin bikin babbar sallar