Buhari ya jinjina wa kungiyar Izala
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa kungiyar Addinin Musuluncin nan ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah bisa kokarin da take yi ba dare ba rana wajen wa’azantar da al’ummar kasar nan da kasashen ketare domin su fahimci addini tare da jawo hankulansu kan zaman lafiya. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin […]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa kungiyar Addinin Musuluncin nan ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah bisa kokarin da take yi ba dare ba rana wajen wa’azantar da al’ummar kasar nan da kasashen ketare domin su fahimci addini tare da jawo hankulansu kan zaman lafiya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, wanda ya wakilce shi wurin Babban Taron Shekara da kungiyar ta shirya karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir domin wa’azi da kaddamar da gidauniyar bunkasa ilimi da ilmintarwa na kungiyar a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata a Abuja.
Shugaban kasar ya kara gode wa al’aummar Najeriya bisa yadda suka nuna damuwarsu tare da yi masa addu’o’i a lokacin da ya yi fama da rashin lafiya. Sannan ya roki jama’a su ci gaba da yi masa addu’a don ganin ya cimma kudirorinsa na ciyar da kasar nan gaba.
A jawabin Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce kungiyar tana matukar farin ciki da samun Gwamnatin Buhari a kasar nan, kasancewar ya tabbatar da tsaro. “Kuma soyayyar da nake yi wa Buhari ba ta kudi ba ce, sai don Allah. Kuma shi ne Shugaba na farko a tarihi da tun kafin a rantsar da shi barayin gwamnati suka fara maido abin da suka sata,” inji Sheikh Jingir.
Sheikh Jingir ya ce zuwa yanzu, kungiyar tana da makarantu 6,144 da dalibai sama da miliyan 7 a Najeriya. Yana mai cewa “Babu abin da za mu bai wa al’umma ya taimake su kamar ilimi, shi ya sanya wannan kungiya ta tashi tsaye wajen bunkasa ilimi a Najeriya da kasashen makwabta. Tuni mun rubuta takarda a ba mu izini mu bude jami’a kuma an ba mu ka’idoji a zamanin wannan gwamnati ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Muna rokon gwamnatin ta ba mu goyon baya kan wannan kudiri namu na bude wannan jami’a.”
A jawabin, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmi ne kan su hada kai su zauna lafiya, domin sai da zaman lafiya ne ake iya yin komai na rayuwa. Sarkin Musulmin wanda Mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Usman Chido Yamusa ya wakilta, ya yi kira ga al’ummar Musulmi su tashi su nemi ilimi, musamman ilimin addini da na kimiyya da kere-kere. Ya ce babu shakka al’ummar Musulmi suna yin sakaci kan harkokin ilimi a Najeriya. Sai ya yaba wa kungiyar Izala bisa yadda ta kakkafa makarantu a birane da kauyuka.
Taron wanda ya kunshi kaddamar da littafin tarihin kungiyar wanda Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya wallafa ya samu halartar manyan baki da suka hada da Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello da Sanata Isah Maina da ya wakilci Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambul da tsohon Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Babangida Aliyu da manyan malamai da ’ya’yan kungiyar daga ciki da wajen Najeriya.