Buhari Ya Jinjina Wa Sarkin Musulmi Kan Wanzar Da Zaman Lafiya

Shugaba Buhari ya mika ka sakon gaisuwarsa ga Mai Alfarama Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku a bisa cikar sa shekaru 66 da haihuwa. Sakon gaisuwar daga Fadar Shugaban Kasa ta fito ne ta hannun hadimin shugaban, Femi Adesina, a ranar Laraba. Gwamnati za ta ba da kwangilar tsaron Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Matar mai […]

Buhari Ya Jinjina Wa Sarkin Musulmi Kan Wanzar Da Zaman Lafiya

Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya.

Shugaba Buhari ya mika ka sakon gaisuwarsa ga Mai Alfarama Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku a bisa cikar sa shekaru 66 da haihuwa.

Sakon gaisuwar daga Fadar Shugaban Kasa ta fito ne ta hannun hadimin shugaban, Femi Adesina, a ranar Laraba.

Shugaba Buhari y yaba wa Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya bisa kokarinsa na wanzar da zaman lafiya da kuma hadin kai ta hanyar tuntubar juna.

Ya kuma bayyana cewa sarkin ya dore da yin hakan tun nadinsa zuwa kan karagar mulki a Shekarar 2006.

Shugaba Buhari ya yi masa addu’ar karin lafiya da jimirin aiki da jama.

A ranar Laraba, 24 ga watan Agusta, 2022 ne Sarkin Musulum, Muhammad Sa’ad Abubakar ya cika shekara 66 a duniya.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara