Buhari ya kaddamar da aikin bututun iskar gas a Arewa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas mai tsawon kilomita 614 a Arewacin Najeriya. Bututun iskar gas din mai suna AKK zai taso daga Ajaokuta a jihar Kogi, ya biya ta Abuja, zuwa Kaduna, ya karasa zuwa Kano. Gwamna Akeredolu na Ondo ya kamu da COVID-19 Shaikh Dahiru Bauchi ya […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas mai tsawon kilomita 614 a Arewacin Najeriya.
Bututun iskar gas din mai suna AKK zai taso daga Ajaokuta a jihar Kogi, ya biya ta Abuja, zuwa Kaduna, ya karasa zuwa Kano.
- Gwamna Akeredolu na Ondo ya kamu da COVID-19
- Shaikh Dahiru Bauchi ya ja layi da gwamnoni kan almajirci
Da yake lura da kaddamar da aikin ta fasahar taro na videoconference a ranar Talata daga Fadar Gwamnati a Abuja, Buhari ya ce shimfida bututun abu ne mai muhimmanci ga ‘yan Najeriya, don haka ba za a bari ya lalace ba.
Buhari wanda ya ce aikin zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin Najeriya ya ce wajibi ne a yi dukkan mai yiwuwa wajen aiwatar da aikin yadda aka tsara shi, a kuma kammala shi a kan kari.
An bude aikin ne daga kusurwa biyu, inda Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya wakilci Buhari ta bangaren Ajaokuta tare da Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari.
A daya bangaren Kuma, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna sun kaddamar da aikin daga Rikachikun tare da Karamin Ministan Albarkatun Mai.