Buhari ya kaddamar da tambarin tunawa da ’yan mazan jiya

Ya yi alkawarin biyan bukatun sojoji domin tabbatar da tsaro da dorewar Najeriya a dunkule

Buhari ya kaddamar da tambarin tunawa da ’yan mazan jiya

Shugaba Buhari ya kaddamar da tambarin tunawa da ’yan mazan jiya na bana da gudunmuwar Naira miliyan 10 a madadin Gwamnatin Tarayya.

Buhari ya yi hakan ne a wani kwarya-kwaryan bikin da ya gudana a Fadar Shugaban Kasa kafin fara taro Majalisar Zartarwa ta kasa a ranar Alhamis.

Buhari ya roki jama’ar Najeriya da su guji yin kalaman da za su raba kawunansu ko yin barazana ga tsaron kasar.

Ya ce bikin tunawa ne ‘yan Najeriya da suka sadaukar da rayukansu saboda kasar a lokuta daban-daban domin dorewarta.

Shugagaban Kasar ya jinjina wa sojojin Najeriya kan yadda suka dage wajen tabbatar da kasancewar Najeriyar kasa daya dunkulalliya duk da barazanar COVID-19.

Ya kuma yi alkawarin biyan bukatun sojoji domin ayyukansu na tabbatar da tsaro da zaman lafiya wanda ya ce gwamnatinsa ta ba wa matukar muhimmanci.

Mahalarta zaman sun hada da mataimakinsa, Yemi Osinbajo; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan; Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila; da Shugaban Hukumar Huldar Kasashen Ketare.

Saurran mahalarta su ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno; da kuma Shugabar Ma’aikatan Gwamantin Tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan.

Sauran su ne Shugaba da kuma Sakataren Kungiyar Tsoffin Sojoji da kuma shugabannin hukuomin tsaro.

A lokacin bikin Buhari ya ba wa Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) Isa Kwarra, rantsuwar kama aiki.

Kwamishinonin NPC da suka karbi ratsuwar su ne Ibrahim Mohammed (Bauchi); Ayodeji Ajayi (Ekiti),  Joseph Kwai Shazin (Birnin Tarayya) da kuma Garba A. Garba (Jigawa).

Akwai kuma Bala Almu Banya (Katsina); Alhaji Razaq Gidado (Kwara); Mrs Bimbola Salu-Hundeyin (Lagos), sai kuma Ali Silas Agara (Nasarawa).

Sauran su ne Chuso A. Dottijo (Sokoto); Mai Aliyu Mohammad (Yobe), da kuma Muhammadu  Muktar Rini (Zamfara).