Buhari ya kaddamar da yaki da barayin shanu a Zamfara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri mai taken ‘Operation Harbin Kunama’ domin yaki da barayin shanu da ’yan fashi da makami a dajin dansadau da ke Jihar Zamfara, inda ya ce tabbatar da zaman lafiya a kasar nan shi ne babban abin da gwamnatinsa ta fi bai wa fiffiko.Manufar ita ce a […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri mai taken ‘Operation Harbin Kunama’ domin yaki da barayin shanu da ’yan fashi da makami a dajin dansadau da ke Jihar Zamfara, inda ya ce tabbatar da zaman lafiya a kasar nan shi ne babban abin da gwamnatinsa ta fi bai wa fiffiko.
Manufar ita ce a fatattaki ’yan bindiga da barayin shanu da suke addabar manoma da makiyayan jihar.
Masarautar dansadau da ke karamar Hukumar Maru tana daya daga cikin yankunan da suka fi fama da tashin hankali a sanadiyar ’yan bindiga da barayin shanu. A watan Afrilun shekarar 2014, ’yan bindiga sun kashe sama da mutum 100 a kauyen ’Yargaladima da ke kilomita 20 yamma da dansadau.
Buhari, wanda ya isa wurin taron a helikwabtan sojojin sama tare da Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da manyan jami’an gwamnati da misalin karfe 5:00 na yamma, ya gana da manyan hafsoshin sojoji kafin ya yi jawabi ga sojojin musamman da aka tura yankin don aiwatar da shirin.
A takaitacccen jawabinsa ga sojojin da aka tura cikin dajin, Shugaban ya ce ya dade rabonsa da ganin atisayen da ya tsaru irin wannan na dansadau.
Ya ce, tun kafin zabe, sun gano harkar tsaro da tattalin arziki da yaki da cin hanci a matsayin abubuwa uku da ke da muhimmanci sosai ga ci gaban kasa, wadanda babu wanda yake musun haka.
A jawabin, Hafsan Hafsoshin Sojojin kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce harkar tsaro ta lalace sosai a baya ne saboda nuna halin ko in kula daga shugabannin da suka gabata.
Gwamnan Abdul’aziz Yari, ya ce mayakan za su zauna a cikin dajin har sai sun fatattaki masu tayar da hankali da ke cikin dajin.
Gwamna Aminu Masari na Katsina ya shaida wa wakilinmu cewa wannan yakin da aka kaddamar yana da matukar muhimmaci ga jiharsa saboda wannan dajin yana da dangana da kananan hukumomi takwas na Jihar Katsina.
Ya ce, barayin shanun sun fara guduwa domin tsoron sojojin da za a turo kuma jami’an tsaro a Jihar Katsina sun fara kama wasunsu.