Buhari ya kadu da mutuwar sarauniyar kyau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna kaduwa tare da alhininsa biyo bayan mutuwar tsohuwar Sarauniyar Kyau Ibidun Itua-Ighodalo, mai dakin Shugaban Cocin Tiriniti da ke Legas, Fasto Itua Ighodalo. A sanarwar da Mai Taimaka wa Shugaba Buhari a kan Harkokin Yada Labarai da Al’amuran Hulda da Jama’a Femi Adesina ya fitar a ranar Lahadi, 14 […]

Buhari ya kadu da mutuwar sarauniyar kyau

Tsohuwar Sarauniyar Kyau Marigayiya Ibidun Itua-Ighodalo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna kaduwa tare da alhininsa biyo bayan mutuwar tsohuwar Sarauniyar Kyau Ibidun Itua-Ighodalo, mai dakin Shugaban Cocin Tiriniti da ke Legas, Fasto Itua Ighodalo.

A sanarwar da Mai Taimaka wa Shugaba Buhari a kan Harkokin Yada Labarai da Al’amuran Hulda da Jama’a Femi Adesina ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, ya ce Shugaba Buhari ya girgiza da mutuwar, inda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar da kuma daukacin mambobin cocin na Tiriniti.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari yana sane da cewa Fasto Ighodalo na cikin mutanen da ke yi wa Najeriya addu’a kuma ya aike masa da sakon ta’aziyya a lokacin da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Malam Abba Kyari ya rasu.

“Muna fatan za ku karbi ta’aziyyarmu, Allah Ya ba ku hakurin jure wannan rashi, Ya ba ku kwarin gwiwa a wannan lokaci da Ya jarabce ku”, inji sanarwar.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara