Buhari ya karbi gurguwar shawara kan taron NEC —APC
Shugabannin Jam’iyyar APC na kasa na zargin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da karbar gurguwar shawara wurin amsa gayyatar abin da suka kira ‘haramtaccen’ taron Kwamitin Zartarwan Jam’iyyar na Kasa (NEC) wanda Victor Giadom, ‘shugaban bangare na jam’iyar’ ya kira. A ranar Laraba ne dai Kakakin Shugaban Kasar Garba Shehu ya ce Buhari zai halarci taron, […]
Shugabannin Jam’iyyar APC na kasa na zargin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da karbar gurguwar shawara wurin amsa gayyatar abin da suka kira ‘haramtaccen’ taron Kwamitin Zartarwan Jam’iyyar na Kasa (NEC) wanda Victor Giadom, ‘shugaban bangare na jam’iyar’ ya kira.
A ranar Laraba ne dai Kakakin Shugaban Kasar Garba Shehu ya ce Buhari zai halarci taron, sakamakon samun shawarwarin kwararru da ke tabbatar da halascin shugabancin Giadom a jam’iyyar.
Kwamitin Gudanarwan APC na Kasa (NWC), na zargin an yi wa Buhari shigo-shigo-ba-zurfi har ya amince ya halarci taron da Victor Giadom wanda ke da’awar shugabantar jam’iyyar ya kira a ranar Alhamis 25 ga watan Yunin da muke ciki.
Shugabancin jam’iyyar na kasa a cikin wata sanarwar ya ce, “Kwamitin Gudanarwar na Kasa (NWC) na watsi da gayyatar haramtaccen Taron Kwamitin Zartarwar na Kasa (NEC) da wani Cif Giadom ya kira. Mun yi amannar cewa halartar taron goyon bayan karya doka ne da kuma zura ido ga masu saba wa Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyarmu”.
- Rikicin shugabanci: ’Yan sanda sun rufe hedikwatar APC
- Buhari ya amince da shugabancin Giadom a APC
- Kotu ta takadar da Giadom daga jam’iyyar APC
- Babu mafita ga rikicin APC sai abu daya —Giadom
Ana ganin tsoma bakin Fadar Shugaban Kasa a rikicin shugabancin jam’iyyar tamkar Buharin ya raba gari ne da Uban Jam’iyyar na Kasa Bola Tinubu da kuma NWC da ya daktar da Giadom wanda ake ganin yana da goyon bayan gwamnonin jam’iyyar.
NWC ta dakatar da Giadom
NWC din APC dai ya riga ta dakatar da Giadom bayan ya fara da’awar zama shugaban jam’iyyar sakamakon dakatar da Adams Oshiomhole da kotu ta yi a matsayin shugabanta na kasa. Bayan dakatar da Oshiomhole, uwar jam’iyyar ta nada Abiola Ajimobi wanda rashin lafiyarsa ta sa Prince Hilliard Eta ke aiki a matsayin mukkadashinsa.
Ayyana kasa da Giadom ya yi a gurbin Oshiomhole bayan ya samu umarnin kotu a kan hakan ta sa jam’iyyar dakatar da shi bisa zargin haddasa fitina, ta kuma maye gurbinsa da Worgu Boms a matsayin Mataimakin Sakatarenta na Kasa.
Giadom ya kira taron NEC, Buhari zai halarta
Bayan haka ne a ranar Talata Giadom ya kira taron NEC wanda ya ce da sanin Shugaba Buhari za a yi domin warware matsalolin jam’iyyar, yana mai watsi da dakatawar da jam’iyyar ta yi masa a matsayin abin dariya.
Bayan jam’iyyar ta yi watsi da taron nasa ne a ranar Laraba Fadar Shugaban Kasa ta bakin Garba Shehu ta ce Buhari zai halarci taron saboda gamsuwarsa da halascin shugabancin Giadom.
An yi wa Buhari kumbiya-kumbiya, inji NWC
Sanarwar da Hilliard Eta da kuma Sakataren na Riko Arc. Waziri Bulama suka fitar ta yi fatali da taron, tare da zargin an yi wa Shugaba Buhari ingiza mai kantu ruwa, don haka suka bukaci ya binciki gaskiyar lamarin.
“Da haka ne zai fahimci cewa taron da wani mai suna Cif Victo Giadom ya saba doka kuma babban laifi ne”, inji sanarwar.
Abin jira a gani shi ne ko Buharin zai halarci taron.