Buhari ya karbi maganin coronavirus daga Madagascar
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi maganin COVID-19 wanda aka hada a Madagascar, yana jaddada cewa zai nemi shawarar masana kimiyya kafin ya bari a yi amfani a kan ’yan Najeriya. Shugaban ya fadi haka ne ranar Asabar lokacin da yake tattaunawa da Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Gini Bisau wanda ya taho da samfurin maganin […]
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi maganin COVID-19 wanda aka hada a Madagascar, yana jaddada cewa zai nemi shawarar masana kimiyya kafin ya bari a yi amfani a kan ’yan Najeriya.
Shugaban ya fadi haka ne ranar Asabar lokacin da yake tattaunawa da Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Gini Bisau wanda ya taho da samfurin maganin da Madagascar ta bai wa kasashen Afirka.
Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun babban mai ba da shawara ga shugaban kasa a kan al’amuran yada labarai, Malam Garba Shehu, ta ambato Buhari yana cewa matsayinsa a kan dukkan magungunan gargajiya ko saiwoyi bai sauya ba.
- Buhari ya umarci a shigo da maganin coronavirus daga Madagascar
- ‘Ba za mu yarda da gwajin maganin coronavirus a Kano ba’
“Muna da cibiyoyinmu, da tsare-tsarenmu a kasar nan. Duk wani hadi irin wannan su ya kamata a kaiwa don su tabbatar.
“Ba zan bari a yi amfani da shi ba, ba tare da amincewar cibiyoyinmu ba”, inji shugaban kasar.
Da yake jawabi game da dalilin zuwansa Najeriya, Shugaba Embalo ya ce ya zo neman shawarar “uba” a wurinsa, Shugaba Buhari, a kan shirinsa na kafa “gwamnatin hadin kan kasa” da kuma yaki da cin hanci da rashawa, inji sanarwar.
“Matsalolin Gini Bisau matsalolin Najeriya ne. Na zo wurinka a matsayina na da a gare ka, ina bukatar taimako don faranta wa al’ummata rai”, inji Mista Embalo.
Da yake mayar da martini ga wadannan bukatun, Shugaba Buhari ya yaba da kwazon Shugaba Embalo wajen samar da kwanciyar hankali da shawo kan ’yan adawa su shiga gwamnatinsa ta hada kan kasa.
A farkon makon nan mai karewa ne dai Shugaba Buhari ya bayar umarnin shigo da kason Najeriya na maganin na Madagascar wanda aka ce an kai Gini Bisau.