Buhari ya karya dokar zabe a ranar zabe

Buhari ya take dokar zabe a bainar jama’a a wurin da kada ya kuri’arsa ranar Asabar.

Buhari ya karya dokar zabe a ranar zabe

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karya dokar zaben da ya sanya wa hannu a bainar jama’a ta hanyar nuna abin da ya zaba a zaben shugaban kasa na 2023.

Bayan Buhari ya kada kuri’arsa a akwatin zabe mai lamba 003 a mazabarsa ta Sarkin Yara da ke mahaifarsa a Daura Jihar Katsina, sai ya daga katinsa na jefa kuri’a yana nuwa da duniya.

Ni zan lashe zaben shugaban kasa —Kwankwaso

An samu lattin zuwan kayan aikin zabe a Abuja

Hakan da ya yi haramun ne a karkashin Dokar Zaben ta 2022 da majalisar dokoki ta kasa ta yi wa kwaskwarima, shi kuma ya sanya hannu ta zama doka a shekarar 2022.

Sashe na 129 (1) na Dokar Zaben ya ce, “Nuna duk wani abu da ke alamta jam’iyya ko mai alaka da zabe a wurin da ake yin zabe ko tattara sakamakon zabe laifi ne da zai jawo wa wanda ya aikata tarar N100,000 ko kuma daurni wata shida a gidan yari.”

Wannan ne dai karon farko da Buhari ya kada kuri’a a matsayin dan kallo tun bayan da a fara zawarcin kujerar shugaban kasa a 2002, shekara 20 da suka gabata.

A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 Buhari zai mika mulki bayan ya kammala wa’adi biyu na shekara akwas da ya fara a shekarar 2015.