Buhari ya kashe wa matattun matatu fiye da kudin gina Matatar Dangote —Gwamnan Nasarawa
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce, rashin aikin matatun man gwamnati ne ya sa ta fara biyan tallafin mai
Kudin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kashe a kan gyaran matatun man gwamnati a shekara takwas na mulkinsa ya fi kudin da aka gina katafariyar matatar mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka, a cewar Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.
Babban attajirin Afirka wanda kuma dan Najeriya ne, Aliko Dangote, ya gina matatar tasa mai karfin samar da tataccen mai ganga 650,000 a kullum a Legas, a cikin shekaru shida, a kan kudi Dala biliyan 19.
Matatar tasa mai komai-da-ruwanka ita ce irinta mafi girma a duniya, kuma ta kusa ninka karfin daukacin matatun mai na gwamnatin Najeriya, wadanda tsawon shekaru ake ta faman ganin sun mike, amma har yanzu shiru.
“Jimillar karfin matatun man gwamanti ganga 450,000 ne a rana, matatar Dangote kuma ganga 650,000, wadda a kan Dala biliyan 19 ya gina.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ciniki ya yi baya a gidajen mai saboda tsadar fetur
- Dambarwa 5 a kwana 10 na sabon Gwamnan Filato
Gwamnatin Buhari ta sha ba da kwangilar gyara matatun mai na Kaduna da Warri da Fatakwal, a kan makudan kudade, amma har ya sauka daga mulki bayan shekara takwas, babu wadda ta tsaya da kafafunta.
Amma duk da haka, gwamnan na Nasarawa ya ce fara aikin Matatar Man Dangote zai taimakawa wajen kawo saukin wahalar man da ake fama da ita a Najeriya.
Game da cire tallafin mai da ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya kuma, Gwamna Abdullahi Sule ya ce, tun da farko rashin aikin matatun man gwamnati ne ya sa gwamnatin ta bullo da biyan tallafin, wanda a duk shekara ke lakume mata daruruwan bilioyin Naira.
A cewarsa, “A bangarenmu, gwamnatinmu ba ta yi abin da ya kamata, ba. Bayan hawan Buhari mulki a 2015 farashin danyen mai ya karye zuwa Dala 30 kuma a lokacin babu tallafi.”
Sai dai, Gwamna Sule, wanda aka yi hirar da shi a tashar Channels, ya koka game da sarkakiyar da ke tattare da kula da matatun mai, wanda “ya kunshi bangaren ruwa da na danyen mai da man dizel, da wasu bangarori akalla biyar da matatar mai take kunsa.
“Idan gwamnati ta ce ta ware wa matatu Dala biliyan biyu a shekara, shugaban kasa bayarwa yake yi, kuma kashe su ake yi a kan matatun.