Buhari ya kawo karshen jita-jitar rashin jituwa tsakanisa da Gwamna Gaidam

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa a Jihar Yobe cewa akwai rashin jituwa a tsakaninsa da Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam bayan da ya mika tutar tsayawa takara ga Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC. Gwamna Gaidam ya karbi tutar ce daga hannun Janar […]

Buhari ya kawo karshen jita-jitar rashin jituwa tsakanisa da Gwamna Gaidam
Buhari ya kawo karshen jita-jitar rashin jituwa tsakanisa da Gwamna Gaidam

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa a Jihar Yobe cewa akwai rashin jituwa a tsakaninsa da Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam bayan da ya mika tutar tsayawa takara ga Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC.

Gwamna Gaidam ya karbi tutar ce daga hannun Janar Buhari a gangamin yakin neman zabe na shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a garin Bauchi a ranar Talatar da ta gabata.
Jinkirin ba da tuta ga Gwamnan ta haifar da maganganu a jihar inda wasu ke cewa an ki ba Gwamnan tutar ce don ba sa ga maciji da Buhari, yayin da wasu ke cewa saboda ya yi rantsuwa a matsayin Gwamna sai biyu ne ya sa Buhari ya ki ba shi tutar.
Wannan jita-jitar ta sa a kwanakin baya Gwamna Gaidam ya musanta cewa Buhari ya ki zuwa jihar ne saboda akwai jikakkiya a tsakaninsu, lokacin da yake jawabi a wurin gangamin karshe na yakin neman zabensa a shiyyar Yobe ta Kudu a filin wasa na 27 Augusta da ke Damaturu.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce, babu rashin jituwa a tsakanina da Janar Buhari domin Janar din ya sha fadin cewa Gwamna Gaidam na cikin mutum uku da yafi amincewa da su, don haka ya kamata masu yada wadannan karerayi su gane cewa, maganganun da suke yi ba gaskiya ba ne.
Gwamna Gaidam ya ce abin da ya hana Janar Buhari zuwa Jihar Yobe don yakin neman zabe shi Gwamnan ne da sauran masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC a jihar suka ce sun yafe masa zuwa “Saboda matsalar tsaro, domin in zai zo Yobe dole sai ya sauka a Maiduguri ya shiga mota zuwa Damaturu, kuma hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ba ta da cikakken tsaro, haka in a Dutse ko Bauchi ya sauka a jirgi ya zo a mota nan kuma akwai nisa, shi ya sa muka ce mun yafe masa ba sai ya zo ba,” inji Gwamnan.
Gwamnan ya ce a zaben shekarar 2011, Janar yana Jam’iyyar CPC su suna Jam’iyyar ANPP amma al’ummar jihar sun kada masa kuri’a da gagarumar rinjaye, to ina ga yanzu da suke cikin jam’iyya daya?