Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura
Tsohon shugaban ya koma gidan da ke Kaduna, bayan shafe shekara biyu a mahaifarsa.

Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya koma gidansa da ke Jihar Kaduna da zama, bayan shafe shekara biyu a Daura, tun bayan barinsa mulki a watan Mayun 2023.
Buhari, ya zaɓi yin rayuwa mai sauƙi bayan kammala wa’adin mulkinsa ba tare da shiga harkokin siyasa ba.
- Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa
- Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki
Ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da manyan jami’an gwamnati zuwa Kaduna.
Daga cikin tawagar da suka yi masa rakiya akwai Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, mataimakan gwamnan Jihar Katsina, Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, wasu tsofaffin ministoci, da wasu daga cikin hadimansa.
A lokacin da yake barin Katsina, jama’a da yawa sun taru don yi wa Buhari fatan alheri.
Daga cikin manyan da suka yi masa rakiya akwai Malam Mamman Daura, Musa Halilu (Dujiman Adamawa), da Bashir Ahmad.
Komawa Kaduna na nufin wani sabon mataki a rayuwarsa bayan shafe shekara biyu a Daura.