Buhari ya kusa komawa Daura – Sabo Gashuwa

Wani matashi kuma kusa a Jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Alhaji Sabo Imam Gashua ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kusa komawa Daura, domin babu yadda za a yi ya ci zaben 2019 muddin ba a gyara kura-kuran da suka dabaibaye gwamnatin tasa ba. Gashua ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya […]

Buhari ya kusa komawa Daura – Sabo Gashuwa

Wani matashi kuma kusa a Jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Alhaji Sabo Imam Gashua ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kusa komawa Daura, domin babu yadda za a yi ya ci zaben 2019 muddin ba a gyara kura-kuran da suka dabaibaye gwamnatin tasa ba. Gashua ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya kai ofishin Aminiya a Abuja wannan makon.

Da yake amsa tambayar ko gwamnatin APC ta samu cigaba bayan shafe fiye da shekaru a mulkin Najeriya. Sai ya ce “Alhamdulillahi mun gode wa Allah da Ya ba mu nasara har Shugaba Buhari ya dare karagar mulki kuma talakawa sun ba mu dukkan gudumawa. Sun yi mana biki, yanzu abinda suke jira a rama mu su, tun da ita siyasa dama biki ce, idan ka min ni kuma in maka. Hakikanin gaskiya ko ba dadi dole a yabi wannan gwamnati saboda gudumawarta a harkar tsaro wadda ta kawo sauyi cikin kankanen lokaci, amma a siyasance tana da kura-kurai ma su dimbin yawa.”

Ko wadanne sakayya yake bukatar talakawan su samu daga wannan biki da aka yi wa gwamnati? Sai ya ce “Da farko dai wajibi ne a taba zuciyar talakawa ta yadda rauwa za ta yi sauki, kama daga kayan abinci, man fetir da kanazir da gas, sannan kuma da kyautata harkokin sufuri. Na biyu ya zama an bude harkokin shigowar samu na tattalin arziki, ta yadda al’umma za su samu ayyukan yi. Kuma babban abin bakin ciki a wannan gwamnati ace a harkar daukar aiki manya ke hada baki sun aba kansu da ‘ya’yansu. Wani lokacin ma zaluncin da ake yi a karkashin wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ya fi wadda PDP ta yi a baya, domin su idan suka dauko jam’iyya da zababbu ta ke baiwa, amma ita APC bare ta ke bai wa,” in ji shi.

Matashin dan siyasar ya ce a kullum farin jinin Muhammadu Buhari kara raguwa ya ke yi, “Kullum magoya bayansa raguwa suke ba karuwa ba, kuma idan aka ci gaba a haka to shiga zabe ba zai mana dadi ba! Sannan mafi yawan wadanda muka taimake shi ya ci zaben ya juwa ma na baya. A lokacin da Obasanjo ya hau mulki cikin mako biyu ya zubar da dukkan mukarraban gwamnatin da ya gada ta Abdulsalami Abubakar ya zuba nasa, amma shi Shugaba Buhari hatta jakadun kasashen waje sai da ya shekara biyu ya nada, fiye da shekara biyu ofisoshin jakadancinmu na kulle. Sannan akwai mukamai 6,500 da ya kamata ya yi, amma har yanzu 1,500 kawai ya yi, saura kimanin 5,000 suna nan mutanen Jonathan ne na PDP akan mukaman har yanzu, wasu kuma an kori mutane an rufe ofisoshin babu kowa.”

Da aka tambaye shi ba ya ganin cewa rashin isassun kadi ne ya kawo haka, “Ban yarda ba! Domin dukkan facakar da gwamnatin PDP ta yi haka wannan gwamnatin ma ta ke yi ba abinda ya canja, haka kuma dukkan cin hanci da rashawa na PDP yanzu ma ana yi a APC, to ina bambancin? Kuma idan ma muka kaddara babu kudin ne, to sai hakan ya sa a bar ‘yan PDP kan mukaman? Wane sako ake isarwa kenan? Sannan ofisoshin da aka rufe din a nada wasu mana a rika ba su daidai abinda gwamnatin za ta iya, sai su ce ba su yarda ba? Gaskiya batun rashin kudi ba uzuri ba ne,” a cewarsa.

A karshe ya ce, “Domin yanzu ina tabbatar ma ka cewa kusan kashi 90 cikin 100 na wadanda suka taimake shi ba ya tare da su. Ya gwammace ya dauko ‘yan PDP da ya bai wa ‘ya’yan jam’iyyarsa ta APC, sai kuma mutanen gidansa kawai. To wannan ba dabara ba ce, kuma ba za ta haifar da da mai ido ba! Kuma maganar gaskiya mafi yawan gwamnoni da ‘yan majalisa da ma ministocinsa ba su tare da shi, kawai lokacin zabe ake jira. Domin muddin aka kara gaba kadan, to za a shiga lokacin ‘ba ka isa ba’ lokacin ‘karya ka ke’ lokacin ‘ba za mu yi ba’, kuma da zarar lokacin ya yi ba a gyara ba, to babu makawa Shugaba Buhari zai tattare nasa-ya-nasa ya koma Daura, domin ba zai ci zaben 2019 ba muddin aka ci gaba da tafiya a haka,” ya karkare.