Buhari ya nada Amokachi Jakadan Kwallon Kafa na Najeriya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan wasan Super Eagles, kuma Mataimakin Kocin Najeriya Mista Daniel Amokachi, a matsayin Jakadan Kwallon Kafa na Najeriya. Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu sneya sanar da haka, cikin wani bayani da ya fitar ranar Talatar da ta gabata. Daniel Amokachi, wanda yana daga cikin ’yan wasan da […]
Daniel Amokachi
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan wasan Super Eagles, kuma Mataimakin Kocin Najeriya Mista Daniel Amokachi, a matsayin Jakadan Kwallon Kafa na Najeriya.
Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu sneya sanar da haka, cikin wani bayani da ya fitar ranar Talatar da ta gabata.
Daniel Amokachi, wanda yana daga cikin ’yan wasan da suka taka wa Najeriya leda suka ci Kofin Nahiyar Afirka a 1994 a kasar Tunisiya, ya kuma kasance cikin ’yan kwallon da suka wakilci Najeriya a gasar Olympics a birnin Atlanta na Amurka inda suka ci lambar zinari a 1996.