Buhari ya nada Dokio shugaban shirin afuwa na Neja Delta
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kana Milland Dixion Dikio (mai ritaya), a matsayin sabon shugaban shirin afuwa a yankin Neja Delta wanda a turance ake kira Amnesty Programme. Sabon nadin da shugaban kasar ya yi zai fara aiki ne tun daga ranar 21 ga watan Agustan 2020. Mai magana da yawun shugaban kasa, […]
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kana Milland Dixion Dikio (mai ritaya), a matsayin sabon shugaban shirin afuwa a yankin Neja Delta wanda a turance ake kira Amnesty Programme.
Sabon nadin da shugaban kasar ya yi zai fara aiki ne tun daga ranar 21 ga watan Agustan 2020.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, shi ne ya hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce nadin da shugaban kasar ya biyo bayan sauke Farfesa Charles Quaker Dokubo daga shugabancin shirin.
Hadimin Shugaban kasar ya ce da wannan ne fadar shugaban kasar take umartar Farfesa Dokubo da ya mika wa Kanar Dikio akalar jagorancin shirin a yayin da take yi masa fatan alheri.
Ana iya tuna cewa a ranar Alhamis, 11 ga watan Yulin 2009, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin na Amnesty Programme, domin yi wa tsofaffin tsagerun Neja Delta afuwa.