Buhari ya ayyana Dongban-Mensem Shugabar Kotun Daukaka Kara

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana Mai Sharia Monica Dongban-Mensem a matsayin Shugabar Kotun Daukaka Kara na riko. Buhari ya sanar da hakan ne a bukatar amincewa da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a mukamin da ya aike wa Majalisar Dattawa. Hadimin Sugaban Kasa a kan Yada Labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da […]

Buhari ya ayyana Dongban-Mensem Shugabar Kotun Daukaka Kara

Sabuwar shugabar kotun daukaka kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana Mai Sharia Monica Dongban-Mensem a matsayin Shugabar Kotun Daukaka Kara na riko.

Buhari ya sanar da hakan ne a bukatar amincewa da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a mukamin da ya aike wa Majalisar Dattawa.

Hadimin Sugaban Kasa a kan Yada Labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a cikin sanarwar da ya fitar a yammacin nan.

Mai Shari’a Dongban-Mensem alkali ce a Kotun Daukaka Kara, wadda Hukumar Kula da Harkokin Sharia ta Kasa (NJC) ta gabatar wa Shugaban Kasa sunanta domin nada ta a mukamin.