Buhari ya nada Farfesa Adesugba shugaban NEPZA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Adesoji Adesugba a matsayin sabon Manajan Darektan Hukumar Kula da Fitar da Kayayakin da Ake Samarwa a Cikin Gida (NEPZA). Sanarwar nadin na kunshe ne a wasikar da Buhari ya aike wa Minista Otunba Adebayo na Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya wadda NEPZA ke karkashinta, a […]

Buhari ya nada Farfesa Adesugba shugaban NEPZA

Farfesa Adesoji Adesugba

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Adesoji Adesugba a matsayin sabon Manajan Darektan Hukumar Kula da Fitar da Kayayakin da Ake Samarwa a Cikin Gida (NEPZA).

Sanarwar nadin na kunshe ne a wasikar da Buhari ya aike wa Minista Otunba Adebayo na Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya wadda NEPZA ke karkashinta, a ranar Talata 26 ga watan Yuni, dauke da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sakataren Yada Labaran Ministan, Julius Toba-Jegede, ya ce Adebayo ya yaba da nadin Farfesa Adesugba, kuma yana da kwarin gwiwa cewa kwarewar sabon shugaban na NEPZA za ta taimaka waje kawo ci gaba da cimma manufofin hukumar.

Farfesa Adesugba lauya ne kuma kwararre a fannin tallata zuba jari da bunkasa tattalin arziki, wanda shi ne abin da yake koyarwa a Kwallejin Roegate da ke birnin Dublin na sakar Ireland. Sannan malamin jami’a ne a kasashen Amurka, Gambia da kuma Switzerland.

Tsohon dan kasuwa ne na kasa da kasa kuma shi ne Mashawarcin Shari’a ga Kungiyar Hukumomin Kasuwanci da Masana’antu da Ma’adinai da Harkar Noma ta Kasa (NACCIMA).