NNPC ya yi nisa da aikin neman danyen mai a Filato
Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce ya fara zurfafa neman danyen mai da iskar gas a kananan hukumomin Wase da Kanam na Jihar Filato. NNPC ya ce Wase da Kanam na daga kwancin Binuwai da ake samun danyen mai da iskar gas wadda ake sa ran za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. […]
Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce ya fara zurfafa neman danyen mai da iskar gas a kananan hukumomin Wase da Kanam na Jihar Filato.
NNPC ya ce Wase da Kanam na daga kwancin Binuwai da ake samun danyen mai da iskar gas wadda ake sa ran za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban Kamfanin Mele Kyari, ne ya bayyana hakan a lokacin ziyarar aiki da Kamfanin ya kai wa Gwamna Simon Lalong a gidan gwamnati da ke a Jos.
Kyari, wanda Shugaban sashen kula da Tunon man fetur na NNPC, Abdullahi Bomai ya wakilta, ya ce kamfanin ya yi gwaje-gwaje da naurorin zamani da suka tabbatar da akwai sinadarin (hydrocarbon) a kwancin Binuwan.
Ya kara da cewa NNPC ya gano wata rijiyar danyen mai mai suna ‘Kolmani discovery’ bayan wadanda ake da su a Neja-Dalta da kuma na yankin Binuwai da za su iya kara samar da wasu miliyoyin gangunan danyen mai.
Da yake jaddada niyyar gwamnati na bayar da hadin kai, Kyari ya yi alkawarin samar da ayyukan yi ga ma’aikatata a fannoni daban-daban har da masu sana’oin hannu, a kananan hukumomin biyu.
A nasa bangaren, Gwamna Lalong, wanda Mataiakinsa Farfesa Sonni Tyoden ya wakilta, ya jijina wa NNPC da namijin kokarin da ya ya yi.
Ya ce Kamfanin, a karkashin Jagorancin Mele Kyari, ya yi kokarin ainun wajen ganuwa da kuma binciko ma’adanai a kwancin na Binuwai.