Buhari ya nada Mohammed Hassan Abdullahi Ministan Muhalli

Shi ne Karamin Minista Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha kafin nada shi babban minista.

Buhari ya nada Mohammed Hassan Abdullahi Ministan Muhalli

Mohammed Hassan Abdullahi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Hassan Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana nadin nasa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada Mohammed H. Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli daga ranar 6 ga Afrilu, 2022.”

Mohammed Hassan Abdullahi wanda lauya ne kuma dan asalin Jihar Nasarawa, shi ne Karamin Minista Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha kafin nada shi babban minista.