Buhari ya nada sabon Kwamandan Hukumar NSCDC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Alhaji Abdullahi Gana Muhammadu a matsayin Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC).Wata sanarwa dauke da sanya kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ta ce Malam Abdullahi Gana Muhammadu ya maye gurbin Dokta Ade Abolurin ne, wanda ya yi ritaya daga aiki.Abdullahi Gana Muhammadu, Mataimakin […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Alhaji Abdullahi Gana Muhammadu a matsayin Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC).
Wata sanarwa dauke da sanya kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ta ce Malam Abdullahi Gana Muhammadu ya maye gurbin Dokta Ade Abolurin ne, wanda ya yi ritaya daga aiki.
Abdullahi Gana Muhammadu, Mataimakin Kwamanda Janar ne na hukumar kafin nada shi a matsayin Kwamanda Janar, kuma an haife shi ne a garin Muye da ke karamar Hukumar Lapai a Jihar Neja.
Sabon Kwamanda Janar din yana da digiri na daya a ilimin sanin halayyar dan Adam daga Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato, sai digiri na biyu kan sanya aiki da doka da shari’ar manyan laifuffuka daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Shugaban kasa Buhari ya yi fatar alheri ga tsohon Kwamanda Janar Dokta Abolurin kan ritayarsa daga aiki.
Tuni dai sabon Kwamanda Janar din na NSCDC ya kama aiki, bayan ya karbi ragamar shugabanci daga Dokta Abolurin