Buhari ya nada shugabannin NNPC da NCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dokta Emmanuel Ibe Kachikwu a matsayin Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na kasa (NNPC) da kuma Farfesa Umaru Garba dambatta a matsayin Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC).Dokta Kachikwu, wanda shi ne Babban Mataimakin Shugaban kuma Babban Mashawarcin Kamfanin main a Eddon-Mobil (a Afirka), ya amshi ragama […]

Buhari ya nada shugabannin NNPC da NCC
Buhari ya nada shugabannin NNPC da NCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dokta Emmanuel Ibe Kachikwu a matsayin Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na kasa (NNPC) da kuma Farfesa Umaru Garba dambatta a matsayin Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC).
Dokta Kachikwu, wanda shi ne Babban Mataimakin Shugaban kuma Babban Mashawarcin Kamfanin main a Eddon-Mobil (a Afirka), ya amshi ragama ne daga Dokta Joseph Thlama Dawha.
Wata sanarwa da ta fito daga fadar Shugaban kasa dauke da sanya hannun Kakakin Shugaban kasar Femi Adesina ce ta bayyana nade-naden.
Dokta Kachikwu ya fito ne daga garin Onicha-Ugbo da je Jihar Delta.
Kuma yana da digiri mai daraja ta kololuwa a fannin shari’a daga Jami’ar Najeriya de ke Nsukka da kuma  Makarantar Shari’a ta Najeriya.
Sabon Shugaban na NNPC kuma yana digiri na biyu da digirin digirgir kan shari’a daga makarantar shari’a ta Harbard Law School.
Ya fara aiki a a bankin Nigerian/American Merchant Bank kafin ya koma kamfanin mai na Tedaco Nigeria Limited, inda ya shafe sherara takwas kafin ya koma Eddon Mobil.
Shugaba Buhari ya kuma amince da nada Farfesa Umaru Garba dambatta a matsayin Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC).
Farfesa dambatta, wanda yake da digirin digirgir a Injiniyan Lantarki ya karbi ragamar shugabancin hukumar ne daga Dokta Eugene Juwah wanda wa’adin shugabancinsa ya kare a ranar 29 ga Yulin bana.
Sabon Shugabn na Hukumar NCC yana kuma da digiri na daya da na biyu a Injiniyar Lantarki.
Wakili ne a kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE) kuma ya sadaukar da kai a aiki har ya zama farfesa a Injiniyar Lantarki a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya kware a Injiniyar Sadarwar Tarho da Bayanai da kuma Kimiyyar Sadarwa.
Farfesa dambatta ya rike mukaman shugabanci a lokuta da dama da suka hada da shugaban sashi da shugaban tsangaya da Daraktan Cibiyar Kimiyyar Bayanai da kuma Shugaban kungiyar Inijiniyoyi ta Najeriya (NSE) reshen Jihar Kano, sai Na’ibin Shugaban Jami’a da kuma Mukaddashin Shugaban Jami’a.
Nadinsa a matsayin shugaban Hukumar NCC zai kasance na shekara biyar ne a zangon farko.