Buhari ya nada Tinubu ya jagoranci sulhu tsakanin ‘yan”yan Jam”iyyar APC

A ci gaba da kokarin hada ‘yan Jam’iyyar APC domin su zama tsintsiya madaurinki daya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya daura nauyin tattaunada da yin sulhu tsakanin ‘yan Jam’iyyar APC a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Babban mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu a sanar da hakan. Ayyukan da Tinubu zai […]

Buhari ya nada Tinubu ya jagoranci sulhu tsakanin ‘yan”yan Jam”iyyar APC

A ci gaba da kokarin hada ‘yan Jam’iyyar APC domin su zama tsintsiya madaurinki daya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya daura nauyin tattaunada da yin sulhu tsakanin ‘yan Jam’iyyar APC a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Babban mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu a sanar da hakan.

Ayyukan da Tinubu zai yi, sun hada da raba gardama tsakanin ‘yan jam’iyyar da rikicin shugabancin jam’iyyar da kuma masu rike da mukamai a wasu jihohin kasar.