Buhari ya nada Yusuf Bichi sabon shugaban hukumar DSS
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta cikin gida (DSS). A wata sanarwa da kakakin fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce nadin sabon shugaban zai fara aiki ne daga yau Juma’a 14 ga watan Satumba 2018. Yusuf Bichi zai karbi ragamar shubancin […]

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta cikin gida (DSS).
A wata sanarwa da kakakin fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce nadin sabon shugaban zai fara aiki ne daga yau Juma’a 14 ga watan Satumba 2018.
Yusuf Bichi zai karbi ragamar shubancin hukumar ne daga hannun mukaddashin shugaban Hukumar Matthew Seiyeifa bayan sauke tsohon shugaban Hukumar Lawal Daura daga mukamin.
Yusuf Bichi kwararren jami’in leken asiri ne ya taba zama daraktan hukumar ta DSS a jihohin Jigawa da Naija da Sokoto da Abia.