Buhari ya bukaci damar karbo sabon bashi

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar karbo sabon bashin Naira biliyan 850 saboda gudanar da wasu aikace-aikace a cikin kasafin kudi na shekarar 2020. Buhari ya mika bukatar hakan ne a wani sako da ya aike wa Majalisar Dattawa wadda shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta a zamanta na ranar Talata. A sakon, Buhari […]

Buhari ya bukaci damar karbo sabon bashi

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar karbo sabon bashin Naira biliyan 850 saboda gudanar da wasu aikace-aikace a cikin kasafin kudi na shekarar 2020.

Buhari ya mika bukatar hakan ne a wani sako da ya aike wa Majalisar Dattawa wadda shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta a zamanta na ranar Talata.

A sakon, Buhari ya bukaci majalisar ta bai wa gwamnati damar tattaro bashin a cikin gida saboda gudanar da aikace-aikacen.

Sakon dai bai ba da bayani a kan aikace-aikacen da za a gudanar ba.

Shugaban majalisar ya umarci kwamitinta na kudi da ya yi aiki tare da Ministar Kudi saboda samo cikakkun bayanai a kan bashin.