Buhari ya nuna alamar sake tsayawa takarar

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shagube daga birnin Abijan a yammacin ranar Talatar da ta gabata cewa ta yi wu ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019. Ya yi shaguben ne yayin da yake ganawa da ’yan Najeriya da ke zaune a kasar Koddebuwa inda yake halartar taron hadin gwiwa tsakanin tarayyar turai da […]

Buhari ya nuna alamar sake tsayawa takarar

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi shagube daga birnin Abijan a yammacin ranar Talatar da ta gabata cewa ta yi wu ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
Ya yi shaguben ne yayin da yake ganawa da ’yan Najeriya da ke zaune a kasar Koddebuwa inda yake halartar taron hadin gwiwa tsakanin tarayyar turai da kungiyar tarayyar Afirka.
Shaguben da Buhari ya yi ya kara fitowa fili ne yayin da ya tafi tare da shugaban jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu a cikin jirgi daya inda suka zaune tare suna raha masu daukar hoto na daukar hotonsu.