Buhari ya rantsar da sabbin manyan sakatarori 12
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin Manyan Sakataron Gwamantin Tarayya guda 12 a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Laraba. Buhari ya kuma rantsar da Kwamishinan Hukuamar Tara Kudaden Shiga ta Tarayya (FIRS) Idahagbon Henry ta takwaransa na Hukumar Raba-daidai ta Tarayya (RMFAC) Usman Hassan. Rantsarwar ta gudana ne kafin fara taron […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin Manyan Sakataron Gwamantin Tarayya guda 12 a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Laraba.
Buhari ya kuma rantsar da Kwamishinan Hukuamar Tara Kudaden Shiga ta Tarayya (FIRS) Idahagbon Henry ta takwaransa na Hukumar Raba-daidai ta Tarayya (RMFAC) Usman Hassan.
Rantsarwar ta gudana ne kafin fara taron wanda shi ne karo na 13 da ake yi a Fadar Shugaban Kasa ta bidiyo, tun bayan bullar cutar coronavirus.
Tun a watan Yuni aka nada sabbin Manyan Sakatarorin, kamar yadda Shugabar Ma’aikatan Gwamantin Tarayya Folasashe Yemi-Esan ta bayyana a lokacin.
Sabbin Manyan Sakatarorin su ne: Alkali Bashir Nura daga Jihar Kano Kano da Ardo Babayo Kumo daga Gombe da kuma Anyanwutaku Adaora lfeoma daga Anambra.
Sauran su ne Hussaini Babangida daga Jigawa, Mohammed Aliyu Ganda daga Sokoto da kuma Mahmuda Mamman daga Yobe.
Akwai kuma Belgore Shuaib Mohammad Lomido daga Jihar Kwara da kuma Akinlade Oluwatoyin daga Jihar Kogi da kuma Ekpa Anthonia Akpabio da Kuros Riba.
Sannan Udoh Moniloja Omokunmi daga Jihar Oyo da Meribole Emmanuel Chukwuemeka daga Jihar Abia sai kuma Tarfa Yerima Peter da ga Adamawa.