Buhari ya rantsar da shugaban RMAFC da wasu Kwamishinoni
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yau Alhamis ya rantsar da shugaban Hukumar tara kudin shiga da raba shi da kuma tsara albashi da hakkokin ma’aikata ta kasa (RMAFC), Elias Mbam da wasu Kwamishinoni 29. A yayin rantsarwar Shugaba Buhari, ya bukaci sabon shugaban Hukumar RMAFC da sauran Kwamishinoni don yin aiki tukuru wajen toshe gibin […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yau Alhamis ya rantsar da shugaban Hukumar tara kudin shiga da raba shi da kuma tsara albashi da hakkokin ma’aikata ta kasa (RMAFC), Elias Mbam da wasu Kwamishinoni 29.
A yayin rantsarwar Shugaba Buhari, ya bukaci sabon shugaban Hukumar RMAFC da sauran Kwamishinoni don yin aiki tukuru wajen toshe gibin da ake samu wajen tara kudaden haraji na asusun gwamnatin tarayya.
Shugaba Buhari, ya kara da cewa, su rike gaskiya wajen gudanar da harkokin su. Kuma ya bayyana musu cewa, gwamnati a shirye take ta fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekara 10, kokarin Hukumar zai taimaka wajen samun nasarar shirin.