Buhari ya sabunta wa’adin Darekta Janar din ITF
Sanarwar karin wa’adin na zuwa ne tun kafin cikar na farko da zai kare a watan Satumba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kara nada Joseph Ntung Ari ya shugabanci asusun raya masana’antu (ITF).
Sabon wa’adin na tsawon shekara hudu da zai fara daga watan Satumba, a cewar Babban Sakataren Ma’aikatar Masana’antu da zuba jari, Nasir Sani Gwarzo.
Ya ce wasikar karin wa’adin daga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ta bukaci ya ci gaba da kyawawan ayyukan hukumar domin cika alkawarin Shugaba Buhari na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci a cikin shekara 10 masu zuwa.
Nasir Gwarzo ya ce Ministan ma’aikatar ya bukaci Darekta Janar din da daukacin ma’aikatan ITF su hada kai domin samun nasara a ayyukan hukumar.
Ya kuma ce masa ya kalli sabon nadin a matsayin karin damar hidimta wa kasa da kuma dorawa a kan nasarorin wa’adinsa na farko.
A shekarar 2016 ne Shugaba Buhari ya fara nada Joseph Ntung Ari ya yi wa’adi da na shekara hudu.