Buhari ya sake lashe zaben shugaban Najeriya karo na biyu
An bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, a jam’iyyar APC inda ya samu kuri’u 15,191,847 wanda hakan zai ba shi damar sake mulkin kasar na karin shekaru hudu masu zuwa. Abokin takararsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u 11,262,978. Shugaban Hukumar Zabe mai zaman […]
An bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, a jam’iyyar APC inda ya samu kuri’u 15,191,847 wanda hakan zai ba shi damar sake mulkin kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.
Abokin takararsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u 11,262,978.
Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta Najeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana sakamakon.