Buhari ya sallami Babachir

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya salami Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawam da kuma Shugaban Hukumar Binciken Najeriya, Ayo Oye. Mataimakin shugaban kasa akan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter. Hakanan kuma, shugaban kasar, ya amince da nada Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnatin. Shi da Babachir […]

Buhari ya sallami Babachir

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya salami Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawam da kuma Shugaban Hukumar Binciken Najeriya, Ayo Oye.

Mataimakin shugaban kasa akan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter.

Hakanan kuma, shugaban kasar, ya amince da nada Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnatin.

Shi da Babachir an dakatar da shi ne a kwanakin baya, bayan an gano wata badakalar da ta wakana wajen aikawa da kayn tallafin da aka tura wa ‘yan gudun hijira a yankin Arewa maso Gabas.