Buhari ya sallami Shugaban Hukumar SSS ya nada sabo

Shugaban kasa Muham-madu Buhari ya salami Daraktan Hukumar Tsaro ta kasa (SSS), Mista Ita Ekpenyong, inda ya maye gurbinsa da Lawal Musa Daura a matsayin sabon shugaban hukumar. A jiya Alhamis ne aka salami Mista Ekpenyong tare da nada magajinsa a wata takarda daga ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya, Mista danladi Kifasi dauke da sanya […]

Buhari ya sallami Shugaban Hukumar SSS ya nada sabo
Buhari ya sallami Shugaban Hukumar SSS ya nada sabo

Shugaban kasa Muham-madu Buhari ya salami Daraktan Hukumar Tsaro ta kasa (SSS), Mista Ita Ekpenyong, inda ya maye gurbinsa da Lawal Musa Daura a matsayin sabon shugaban hukumar.

A jiya Alhamis ne aka salami Mista Ekpenyong tare da nada magajinsa a wata takarda daga ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya, Mista danladi Kifasi dauke da sanya hannun Daraktan Sadarwa a ofishinsa, Haruna Imrana.
Sanarwar ta ce, an haifi Malam Lawal Musa Daura ne a garin Daura a ranar 5 ga Agustan 1953.
Ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga 1977 zuwa 1980.
Kuma ya fara aiki da Hukumar Tsaro ta kasa (SSS) ne a 1982, inda ya kai mukamin darakta.
Ya taba zama Mataimakin Darakta, bangaren sadarwa da Cibiyar Bayar da Umarni a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja daga shekarar 2003 zuwa 2007.
Kuma ya yi aiki a matsayin Daraktan Hukumar SSS a jihohin Kano da Sakkwato da Edo da Legas da Osun da kuma Imo.
Ya halarci kwasa-kwasai na kwarewa a ciki da wajen kasar nan, ciki har da Cibiyar Nazarin Bukatun kasa Tsare-Tsare (NIPSS) da ke Kuru a kusa da Jos.
Sanarwar ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.