Buhari ya samar da ayyuka 12m a bangaren noma —Garba Shehu

Garba Shehu ya ce a gwamnatin Buhari Najeriya ta wadatu da abinci

Buhari ya samar da ayyuka 12m a bangaren noma —Garba Shehu

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu. (Hoto: www.signalng.com)

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce a bangaren noma kadai Shugaba Muhammadu Buhari ya samar da sabbin ayyukan yi miliyan 12.

Garba Shehu, a yayin wata hira da tashar talabijin, ya ce Gwamnatin Buhari ya yi rawar gani a bangaren tsaro da wutar lantarki da yaki da rashawa da sauransu.

“A bangaren noma kadai Kungiyar Manonman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) na da mutum miliyan 12.

“Sannan a lokacin da gwamnatin nan ta karbi mulki masana’antun takin zamani hudu ne kawai a kasar nan, amma yanzu sun kai 52 kuma su ke samar da takin zamani ga wadannan sabbin manoman shinkafa miliyan 12 a cikin gida.

“Kasar nan ta wadatu da abinci, sannan an kara yawan bangarorin tattalin arziki da gwamnati ke samun kudaden shiga, ba da danyen mai kadai ake dogara ba.

“Kafin zuwanmu a kullum Najeriya na kashe Dala biliyan biyar wajen shigo da shinkafa, amma yanzu ko Dala daya Babban Bankin Najeriya (CBN) ba ya bayarwa don shigo da shinkafa,” in ji shi.

Yaki da rashawa

A bangaren yaki da rashawa kuma, Garba Shehu ya ce babu inda Buhari ya boye kudaden sata, ballantana ya ji tsoron a gurfanar da shi bayan ya sauka daga mulki.

“A matsayina na kakakinsa, hankalina kwance nake yin barci ba na fargabar wani a Najeriya ko kasar waje zai ce min sun gano asusu bankin mai gidana makare da makudan kudade. Ba dai Buhari ba; ya yi hannun riga da badakala,” in ji Garba Shehu.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi