Buhari ya samu kyakkyawar tarba a kasar Japan
A yau Litinin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Japan domin halartar taron kasa da kasa kan bunkasa nahiyar Afirka karo na bakwai, da ake yi wa take da TICAD7 da za a gudanar a birnin Tokyo. Za a gudanar da taron mai taken ‘Africa and Yokohama, Sharing Passion for the Future’, a birnin […]
A yau Litinin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Japan domin halartar taron kasa da kasa kan bunkasa nahiyar Afirka karo na bakwai, da ake yi wa take da TICAD7 da za a gudanar a birnin Tokyo.

Za a gudanar da taron mai taken ‘Africa and Yokohama, Sharing Passion for the Future’, a birnin Tokohama daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Agusta 2019. A yayin da shugaban ya isa kasar, mata da maza ‘yan Japan sun yi shigar gargajiya da aka fi yi a kasar Hausa da yi wa shugaban kasar kyakyawar tarba.
Shugaba Buhari, ya isa kasar Japan ne tare da Gwamnan Benuwe Samuel Ortom da Ministan harkokin kasahen waje Geoffrey Onyeama da Ambasadan Japan a Najeriya Mohammed Gana Yisa da dai sauran su.