Buhari ya shiga tsakani don sasanta Ganduje da Kwankwaso
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC sun shiga domin sansanta rigimar da ta taso a tsakanin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da magabacinsa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.Bayanai sun ce Shugaban kasar ne ya sanya gwamnonin jihohin APC daga Arewa maso Yamma suka gudanar da taro tare da Ganduje da Kwankwaso a gidan […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC sun shiga domin sansanta rigimar da ta taso a tsakanin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da magabacinsa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Bayanai sun ce Shugaban kasar ne ya sanya gwamnonin jihohin APC daga Arewa maso Yamma suka gudanar da taro tare da Ganduje da Kwankwaso a gidan Kwankwaso da ke Abuja, inda aka warware wasu ‘muhimman batutuwa.
Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara ne ya jagoranci sauran gwamnonin da suka hada da Nasir el-Rufa’i (Kaduna) da Badaru Abubakar (Jigawa) da Aminu Tambuwal (Sakkwato) da Aminu Masari (Katsina) da kuma Atiku Bagudu (Kebbi).
an fara ganawar ce da misalin karfe 9:00 na dare zuwa karfe 3:00 na dare, inda Gwamna Yari ya bayar da sanarwar ’yan siyasar biyu daga Kano sun amince su yi aiki tare.
Wata majiya ta kusa da taron ta ce Shugaba Buhari yana ganin yana da muhimmanci ya sanya baki kan batun domin kyale hakan ya ci gaba na iya watsuwa zuwa sauran wurare, lamarin da ba zai haifar wa Jam’iyyar APC ido ba.
Shugaban Ma’aikata na Kwankwaso, Aminu Abdulsalam, wanda ya tabbatar da cewa an gudanar da taron, ya ce an gudanar da shi ne sakamakon tsoma baki masu ruwa da tsaki daban-daban, kuma maigidansa ya amince ya yi aiki tare da Ganduje.
Kakakin Gwamna Ganduje, Malam Baba Halilu dantiye, wanda ya sako wasu hotunan taron ya ce manyan ’yan siyasar biyu sun mayar da wukakensu kube.
Sai dai kuma bayan ’yan awanni da kulla yarjejeniyar, sai wata barakar ta kunno kai, inda wani babban ayari daga Jihar Kano suka mika wata wasika ga hedkwatar Jam’iyyar APC dauke da matsayar da APC ta dauka a jihar na sauke shugabanta, Umar Haruna Doguwa da tsohon Sakataren Tsare-Tsare na Jihar, Sunusi Sirajo.
A gabatarwar Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar (PRO), Bashir Yahaya, ya ce an sauke jami’an biyu ne sakamakon warware matsayar jam’iyyar na a ladabtar da tsohon Gwamnan.
Ya ce an nada Abdullahi Abbas Sunusi a matsayin shugaban riko, yayin da mataimakin sakataren tsare-tsare, Ahmed Muhammad, ya zama mukaddashin sakataren tsare-tsaren.
A jawabin Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Cif John Odigie-Oyegun, ya bayyana takaddamar da “abin bakin ciki,” da bai kamata ba, kuma kawar da hankalin da za a iya magancewa.”
Sai ya roki wakilan su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, inda ya ce gwamnati daya take Jihar Kano da wajibi ne a girmama ikonta. Ya ce jam’iyyar ta kafa wani kwamitin mutum uku a karkashin jagorancin Mataimakin Shugabanta na kasa da Sakatarenta na kasa da Sakataren Tsare-Tsare domin dawo da
Ya ce bai kamata a bari lamarain ya tabarbare ba, akwai bukatar a yayyafa ruwa ga kurar saboda muhimmanci da Jihar Kano take da shi a siyasance.
Ya ce sakatariyar jam’iyyar ta kasa za ta tabbatar wanna takaddama da ta taso a tsakanin fitattun ’ya’yan jihar biyu ba ta kara tabarbarewa ko ta zama batun da za a ruka cece-ku-ce a kafafen watsa labarai ba. “Bai kamata wani daga cikinmu ya yi wani abu da zai dada lalata al’amura ba,” inji shi.
Wakilan sun hada da Shugaban Majalisar Kano da wakilan majalisar 36 daga cikin 40 da shugaban kwamitin dattawan jam’iyar da sauransu.
A wata talla da Shugaban Ma’aikata na Kwankwaso Kwamared Abdulsalam ya fitar a ranar Talata ya yi Allah wadai da sauke Haruna Doguwa da Sunusi Suraj daga mukamansu tare kuma da kama Dokta Yunusa dangwani, tsohon Kwamishina Albarkatun Ruwa bisa zarginsa da yunkurin shirya wani gangamin siyasa don girmama Kwankwaso, lamarin da ke nuna har yanzu kura ba ta lafa ba.