Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekara 50

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, murnar cika shekara 50 tare da yi masa addu’ar samun karin lafiya da basira. Sakon taya murnar da Buhari ya aike ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, ta jinjina wa sarkin bisa kokarinsa wajen wayar da kan al’ummar masarautarsa game da abin da ya shafi rayuwarsu […]

Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekara 50

Mai Martaba Sarkin Bauhi Alhaji Rilwanu Adamu

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, murnar cika shekara 50 tare da yi masa addu’ar samun karin lafiya da basira.

Sakon taya murnar da Buhari ya aike ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, ta jinjina wa sarkin bisa kokarinsa wajen wayar da kan al’ummar masarautarsa game da abin da ya shafi rayuwarsu musamman a lokcin annobar COVID-19.

Buhari ya ce sarkin ya zama abin koyi wajen taimakon jama’a da kuma wanzar da hadin kai da hukuri da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

Shugaban kasar ya ce kokarin sarkin karfafa wa matasa gwiwar rungumar neman ilimi da sana’o’in dogaro da kai abin yabawa ne.

Ya kuma taya iyalai da masoya a da abonkan sarkin da ma daukacin jama’ar Masarautar Bauchi murnar cikar Sarkin shekara 50 a duniya.

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo