Buhari ya taya zababben Gwamna Bayelsa murna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya dan takarar Gwamnan Bayelsa David Lyon, na jam’iyyar APC murnar lashe zaben da aka yi ranar Asabar 16 ga Nuwamba 2019. Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina, ne ya sanar da sakon Shugaba Buhari, ya kuma godewa mambobin jam’iyyar APC wajen gudanar da zaben jihar. Shugaba Buhari, ya yi Allah […]

Buhari ya taya zababben Gwamna Bayelsa murna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya dan takarar Gwamnan Bayelsa David Lyon, na jam’iyyar APC murnar lashe zaben da aka yi ranar Asabar 16 ga Nuwamba 2019.

Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina, ne ya sanar da sakon Shugaba Buhari, ya kuma godewa mambobin jam’iyyar APC wajen gudanar da zaben jihar.

Shugaba Buhari, ya yi Allah Wadai da rasa rayukan da aka yi a jihar Bayelsa lokacin zaben kuma ya mika saon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu.