Buhari ya tsallake waigin hana shi takara

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya tsallake waigin hana shi tsayawa takara, bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage yanke hukunci kan karar da ke nema a haramta damar yin takara zuwa ranar 22 ga watan gobe.  Wasu ’yan siysa ne suka bukaci kotun ta hana […]

Buhari ya tsallake waigin hana shi takara
Buhari ya tsallake waigin hana shi takara

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya tsallake waigin hana shi tsayawa takara, bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage yanke hukunci kan karar da ke nema a haramta damar yin takara zuwa ranar 22 ga watan gobe. 

Wasu ’yan siysa ne suka bukaci kotun ta hana Buhari tsayawa takara bisa zarginsa da rashin takardar kammala karatun sakandare da kuma zarginsa da hannu a tashin hankalin da aka yi bayan zaben shekarar 2011.
A ranar Talata ce Alkalin Kotun Mai shari’a Adeniyi Ademola ya shirya yanke hukunci kan wasu bukatu game da karar, amma sai ya dage zuwa shekaranjiya Laraba, inda a zaman kotun ya sake dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan gobe, wato kusan wata daya bayan zaben.
An rika dar-dar a sassan kasar nan, kan yiwuwar kotun ta haramta wa Buhari tsayawa takara a zaben na gobe Asabar, inda aka rika yada jita-jitar cewa ana matsa wa kotun ta hana Buhari tsayawa takarar.
Kotun ta kuma yi watsi da bukatar da wasu mutum biyu suka gabatar suna neman a hada da su a matsayin wadanda ake kara. daya daga cikin masu wannan bukata shi ne wani dan rajin kare dimokuradiyya, Ebun-Olu Adegboruwa.
A zaman kotun na ranar Talata Mike Ozekhome, wani Babban Lauyan Najeriya kuma lauyan daya daga cikin masu kara mai suna Chukwunweike Okafor, ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar Mista Adegboruwa da daya mutumin da suke neman a hada da su cikin wadanda ake kara, a shari’ar da ke neman a tabbatar da ingancin karar.
daya daga cikin karar da Okafor yake yi yana kalubalantar cancantar Janar Buhari ta tsayawa takara a zaben, inda ya yi zargin cewa dan takarar na APC ya yi da’awar ya mika takardar kammala makarantarsa ga Hukumar INEC, alhali bai yi hakan ba.
Jam’iyyar APC da Hukumar INEC suna cikin wadanda ake kara. Kuma APC da dan takararta sun nuna rashin amincewa da sauraron karar inda suka ce ba a ba su takardar sammaci ta hanyar da ta kamata ba kamar yadda doka ta nema.
Kuma duk da kotun ta ba Mista Okafor dama ya aika sammacin ta hanyar bugawa a jaridu, lauyan dan takarar APC, Wole Olanipekun ya mika bukatar a jingine umarnin inda ya ce a saninsa babu wata kara da aka gabatar a gaban kotun balle ta yanke hukunci a kai.
APC da Hukumar INEC sun ce koda ma an mika musu sammaci ta hanyar da ta kamata, batun da ke gaban kotun shi ne sojan gona, wanda a ganinsu babban laifi ne. Sun ce babban laifi kuma ba a fara shari’arsa ta hanyar sammaci kamar na karamin laifi.
Da yake yanke hukunci kan takaddamar Mai shari’a Ademola ya ce kotun za ta saurari rashin amincewar da uwar shari’ar a lokaci guda, inda ya dage sauraron karar zuwa 22 da 23 ga Afrilu mai zuwa.