Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban ’yan sanda
An kara masa wa’adi kwana uku bayan ranar da ya kamata ya yi ritaya daga aiki.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara wa Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Mohammed wa’adin aikinsa da wata uku.
Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi ya sanar da sanar da haka ne a ranar Alhamis, kwana uku bayan cikar wa’adin Shugaban ’yan sandan.
- Rufe masallaci: Sheikh Abduljabbar ya yi raddi ga Gwamnatin Kano
- An girke jami’an tsaro a gidan Sheikh Abduljabbar
- Matakan soyayya da bayaninsu dalla-dalla
- Maganin gargajiya ya kashe yara ya kwantar da mahaifiyarsu a Kano
Ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da ’yan jarida Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Ya ce an kara wa Mohammed Adamu lokacin ne domin a samu isasshiyar damar zabar magajinsa.