‘Buhari ya tsaya kan gaskiyar da aka san shi’
Wani mai kiwon kaji wanda yake da gonar kiwon kaji ta Yankari Farms da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Abdulrahman Lawal ya bukaci sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya kan gaskiyar da aka san shi da ita. Alhaji Abdurrahaman Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, […]
Wani mai kiwon kaji wanda yake da gonar kiwon kaji ta Yankari Farms da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Abdulrahman Lawal ya bukaci sabon Shugaban kasa Muhammadu
Buhari ya tsaya kan gaskiyar da aka san shi da ita.
Alhaji Abdurrahaman Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce babbar matsalar Najeriya ita ce rashin gaskiya, don haka mutanen da suka zabi Buhari, sun zabe shi ne saboda gaskiyar da aka san shi da ita.
Ya ce, idan Shugaba Buhari ya tsaya kan gaskiyar da aka san shi da ita, to, za a magance matsalolin da suke damun kasar nan.
Ya ce zaben Buhari babbar narasa ce ga al’ummar Najeriya baki daya, domin shi mutumin kirki ne kuma mai gaskiya ne. “Shi ya sa tunda aka sanar da cewa shi ya ci wannan zabe aka fara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya,” inji shi.
Ya yi kira ga al’ummar Najeriya kowa ya rike gaskiya ya gyara kansa ya ba sabon shugaban kasar goyon baya da hadin kai domin a samu nasara.