Buhari ya tuhumi sufeto Janar na ’yan sanda kan yin sakaci da ummarninsa

Shugaba Muhammadu Buhari  ya aike da sammaci tare da tuhumar Sufeto Janar na ’yan sanda, Ibrahim Idirs kan zargin yin sakaci da ummarnin da ya bashi na tarewa a Binuwe lokacin da ake tsakiyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.   Shugaban ya tuhumi shugaban rundunar ’yan sandan ne a wata ganawa da ya […]

Buhari ya tuhumi sufeto Janar na ’yan sanda kan yin sakaci da ummarninsa

Shugaba Muhammadu Buhari  ya aike da sammaci tare da tuhumar Sufeto Janar na ’yan sanda, Ibrahim Idirs kan zargin yin sakaci da ummarnin da ya bashi na tarewa a Binuwe lokacin da ake tsakiyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
 
Shugaban ya tuhumi shugaban rundunar ’yan sandan ne a wata ganawa da ya yi da shi ta tsawon minitina 30 a fadarsa.
 
A taron da masu ruwa da tsaki  na jihar Binuwe suka yi da shugaban kasar a ranar Litinin din da ta gabata a garin Makurdi sun fada wa Buhari cewa sufeto Janar din bai zauna a jihar ba kamar yadda ya ummarce shi.
 
Shugaban kasar ya nemi sufeto janar din ya yi masa bayanin dalilin da ya sa ya yi sakaci da ummarnin da ya bashi.
 
Mai taimakawa shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a shi ya tabbatar wa manema labarai aukuwar haka a daren jiya.