Buhari ya umarci a shigo da maganin coronavirus daga Madagascar
Shugaban Muhammadu Buhari ya ba da umarni a je a kwaso wa Najeriya maganin cutar coronavirus da kasar Madagascar ta sarrafa wanda aka ba da rahoton cewa yana da tasiri wajen warkar da cutar. Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana da gwamnatin tarayya ta kafa don yaki da cutar a Najeriya, Boss Mustapha, shi […]
Shugaban Muhammadu Buhari ya ba da umarni a je a kwaso wa Najeriya maganin cutar coronavirus da kasar Madagascar ta sarrafa wanda aka ba da rahoton cewa yana da tasiri wajen warkar da cutar.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana da gwamnatin tarayya ta kafa don yaki da cutar a Najeriya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja yayin jawabin hadin gwiwa karo na 29 da kwamitin ya gudanar.
Aminiya ta rawaito cewa makonni uku da suka gabata shugaban kasar Magadascar, Andry Rajoelina, ya kaddamar da maganin, wanda ya yi amanna yana warkar da masu fama da cutar, a hukumance.
Cibiyar Binciken Kimiyya ta Malagasy ce dai ta jagoranci ta hada maganin, wanda ta yiwa lakabi da COVID Organics.
- COVID-19: An tallafa wa Kano da cibiyar killace mutane ta zamani
- ‘Wani maganin kwarkwata na kashe kwayar coronavirus’
Yayin da yake gabatar da maganin ga manema labarai, Shugaba Rajoelina ya ce ana samun sinadarin hada maganin ne daga tazargade wadda ake nomawa a kasar don maganin zazzabin cizon sauro.
“Dukkan wani bincike da gwaje-gwaje da muka yi sun tabbatar da cewa maganin na da matukar tasiri wajen magance cutar coronavirus a nan Madagascar”, inji Shugaba Rajoelina.
Ya kara da cewa maganin nasu tuni ya warkar da mutane da dama.
Rajoelina, mai shekaru 45 a duniya, ya kuma ce maganin yana warkar da cutar a cikin kwanaki bakwai kacal.
‘Za mu sake bincike…’
Sai dai kuma yayin da yake amsa tambayoyi a kan ko Najeriya ce ta yo odar maganin, Boss Mustapha ya ce kasar ta Madagascar ce tun da farko ta ware wa wasu kasashe kason su na maganin domin su jarraba.
“Shugaban kasar ne ya tura maganin zuwa kasar Gini Bisau, sannan kuma aka ware wani kason ma wasu kasashen.
“Tuni shugaban kasa ya umarce ni da na tsara yadda za mu shigo da maganin, ya kuma yi umarnin da mu tabbatar da gudanar da cikakken bincike a kan duk wani nau’in maganin da aka sarrafa a gida.
“Saboda haka shi ma wannan din za mu yi zuzzurfan bincike kafin fara amfani da shi”, inji Boss Mustapha.
Najeriya ma tana da shi
Yayin da shi ma yake nasa jawabin, Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce Najeriya ma tana da itatuwan da aka yi amfani da su wajen hada maganin (wato tazargade).
Ministan ya ce Cibiyar Bincike a kan Fasahar Harhada Magunguna ta Kasa (NIPRD) za ta yi bincike a kan maganin don tantance sahihancinsa kafin a amince a yi amfani da shi wajen yaki da cutar coronavirus a Najeriya.
Ya kuma ce za a damka maganin ga kwararrun masu bincike don su ga yadda za a iya amfani da shi.
“Mun gano cewa akwai wannan sinadari na tazargade a nan Najeriya, saboda haka za mu yi bincike mu gano ko nau’in namu iri da ya ne da nasu.
“Yayin da daukacin kasashen duniya ke kokarin gano maganin wannan cuta, Najeriya ma ba za a bar mu a baya ba.
“Za mu yi dukkan mai yiwuwa don ganin mu ma mun taka rawar gani a wannan fagen.
“Za mu fara gwadawa da tabbatar da kowanne nau’in magani kafin mu amince a fara amfani da shi a kasarmu”, inji shi.
- Amurka ta gano chloroquine na maganin cutar Coronavirus
- Chloroquine na sha yayin jinyar coronavirus –Gwamnan Bauchi
Mista Ehanire ya kara da cewa kwamitin kar-ta-kwana na gwamnatin tarayya zai ci gaba da karfafa gwiwar duk masu yunkurin sarrafa kayan yaki da cutar a nan gida Najeriya a kan takwarorinsu na kasashen ketare.
Ministan ya ce tuni suka mika sanfuran irin wadannan kayayyaki ga Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) don tabbatar da nagarta da kuma ingancinsu wajen yaki da cutar.
“Saboda haka da zarar mun sami amincewarsu za mu fara amfani da su tun da dai za su fi sauki da saurin samu, gami da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa”, inji ministan.
Gwajin maganin WHO
Bugu da kari, ministan ya ce jihohin Legas da Ogun da Kaduna da Sokoto da Kano da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya tuni suka amince a yi amfani da su wajen gudanar da gwajin maganin cutar kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukata.
WHO ta ce tuni Najeriya ta bi sahun wasu kasashen duniya da suka amince a yi gwajin maganin cutar a kasashensu, yana mai cewa gwajin zai fara nan ba da jimawa ba.
Babbar jami’ar WHO a Najeriya kuma mamba a kwamitin kar-ta-kwana na gwamnatin tarayya, Dokta Fiona Braka, ta shaida wa jaridar Daily Trust a wata tattaunawa cewa Najeriya ta amince ne a yi gwajin maganin cutar ba rigakafinta ba, tun da ya zuwa yanzu ba a gano rigakafin ba tukunna.
Ya zuwa ranar Litinin da daddare dai, sama da mutane miliyan hudu da dubu dari biyu ne suka kamu da cutar, sama da 285,911 kuma aka tabbatar sun mutu, yayin da kuma sama da mutane miliyan daya da rabi suka warke, kamar yadda alkaluman wata cibiya da ke bin diddigin yaduwar cutar a duniya mai suna Worldometer suka tabbatar.